Spread the love


Tsoron sake yaduwar cutar Korona a karo na biyu ya tilasta kasashen duniya dakatar da sufurin jiragen sama tsakaninsu.


Rahoton dawowar COVID-19 ya sa kasashe da dama daukar matakan kariya daga cutar a karo na biyu, ciki har da dakatar da sufurin jiragen sama daga kasa zuwa kasa.
Kasasen da suka dakatar da sufurin jiragen sama nan take sun hada da Indiya da Poland da Norway da Finland da Denmark da Saudi Arebiya.


Sun kuma dakatar da zirga-zirgar jiragensu da ke zuwa kai-tsaye zuwa kasar Ingila saboda gudun shigo da cutar daga Ingilan zuwa kasashensu.


Galibin kasashen sun dakatar da zirga-zirgar jiragen saman ne daga ranar 21 zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2020 a wani mataki na lura da yadda lamarin cutar zai kasance a tsawon lokacin.


Cutar ta dawo a ƙasashen duniya amma ƙsar Amerika ta bayar da sanarwa samun maganin cutar da bayar da kariya.

Managarciya na kallon a Nijeriya ana son kawai ne a giɗaɗa cutar amma ba ta kai wani mizani da za ta sa a sanya mutane a cikin ruɗani da jin tsoro.

    

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *