Spread the love

Kungiyar magoya bayan ɗan takarar kujerar gwamna a zaben 2023 mai zuwa ta bayyana cewar ba wani dan takarar da za su bi a zabe mai zuwa sai wanda ya taka rawar gani wajen cigaban matasan jihar, domin mun gaji da tura mota ta tashi ta bar mu da kura a baya ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani kwarkwaryar taron da ta shirya kan nuna goyon bayanta ga dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Tafa, Suleja da Gawu a garin Suleja karshen makon nan.

Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban Lado Support Organisation Muhammad Musa Zungeru, yace sun hadu dan wayar da kan matasa musamman irin ayyukan da dan majalisar ya yiwa al’ummar da yake wakilta da har wasu matasan yankunan kananan hukumomin jihar suka anfana da su, dan ganin sun tafi akan tafarki daya na tafiyar Hon. Lado Suleja kan takarar kujerar gwamna a zabe mai zuwa.

Yace yanzu kan mage ya waye, domin shigowar Hon. Lado Suleja siyasar Neja muka ga bambanci sosai, ba na tsammanin akwai lungu da sakon da za a ce wani bai anfana ba, ko a bayan nan ya horar da matasa dari da hamsin ilimin kwamfuta wanda bayan sun kammala ya ba su sabbin kwamfutoci da tallafin naira dubu dari wanda jimlatan kowani matashi ya tashi da akallan tallafin sama da dubu dari uku.Wanda bai tsaya nan yanzu haka akwai shirin horar da matasan yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar ta jihar wanda yanzu haka an yi nisa akan shirin, dan haka mutumin da ya fara wannan yanzu muna da tabbacin idan ya zama gwamna lallai ba zai bar matasa kara zube ba.

Injiniya Kabiru Abdulhamid, sakataren LSO a jihar, yace shi mutumin karamar hukumar Tafa ne daya daga cikin yankunan da Honarabul Lado ke wakilta.

Mun gamsu da tafiyarsa saboda irin wakilcin da yake yi mana a majalisa, a zangon sa na farko a majalisa, ya kai matasa ‘yan asalin Suleja, Tafa da Gawu manyan makarantu a kasar Cairo da Indiya, su a kallan saba’in da hudu, ya dauki nauyin jinyar masu lalura hudu masu tsanani bayan aikin tallafin ilimi a makarantun sakandare da faramare, bayan aikin wutan lantarki da gyaran hanyoyin karkara.Mu a tafiyar LSO, za mu cigaba da zakulo ayyukansa ne dan fadakar da jama’a, bisa al’ada akan dauko muna mutanen da ba su san matsolin jihar ba, shi yasa ko sun zo ba sa iya tabuka komai, yanzu wannan lokacin ya kau. Mun damu gaya akan yadda ake barin matasa baya ba wani kwakwaran abinda aka kirkiro a gwamnatance da zai anfane su, amma a wannan karon a shirye mu ke dan yin gwagwarmayar ganin lallai sai mutumin da yasa jihar a gaba, yasan matsalolin jihar da kuma ya bada gudunmawar cigaban al’umma ne za mu marawa baya wajen ganin ya gaji gwamna Abubakar Sani Bello a zaben 2023 mai zuwa.

Matasan sun ce yanzu haka kayan mu na jaka dan fara zagayawa wajen wayar da kan ‘yan uwan mu matasan sauran kananan hukumomin jihar muhimmancin marawa Hon. Lado Suleja baya a wannan zaben da ke tunkarowa, domin aikin na mu ne gaba xaya.Hon. Abubakar Lado Suleja, shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar Suleja, Tafa da Gurara a majalisar wakilai ta kasa, ya taba zama shugaban matasan APC ta kasa kuma tsohon dan gwagwarmayar siyasa ne a jam’iyyar CPC ta adawa a shekarun baya, da yanzu kiraye kiraye sun  yawa akan sa na yin takarar gwamnan Neja bayan kammala wa’adin zango na biyu na mulkin Alhaji Abubakar Sani Bello na jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *