Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar.

Kwamitin yaki da rashawa ta gwamnatin tarayya ta nemi kungiyoyi masu zaman kan su da gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomi da su kara azama wajen yaki da rashawa domin samun ingantacciyar Najeriya.

Babban sakataren PACAC, Farfesa Isah Radda, ne yayi kiran a lokacin gangamin wayar da kai na masu ruwa da tsaki da kwamitin shirya, wanda hadin gwiwa ne da hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) a Minna.

Farfesa Radda ya cigaba da cewar kamar yadda jama’a suka bada shawarwari na janyo hankalin gwamnatin tarayya da na jahohi wajen mayar da hankali kan inganta bangaren ilimi, da ayyukan gwamnati, za mu tabbatar a rahoton mu mun sanarwa gwamnatin tarayta korafe korafen jama’a ta yadda za mu yi aiki gaba daya wajen tsaftace kasar nan daga rashawa.

Ya cigaba da cewar gwamnatin Muhammadu Buhari ta taka rawar gani sosai wajen yaki da rashawa, domin ta samar da hukumomin da ta dorawa alhakin sanya idanu akan matsalolin rashawa, wanda yanzu haka suna aiki kamar yadda ya dace, yanzu haka akwai tsaffin gwamnoni da sanatoci da daidaikun jama’a da ke komar hukumomin.

Radda yace daga cikin nasarorin da aka samu an kwato adadin N192,000,000,00 daga tsoffin ‘yan difulomasiyya, sannan an kwato N15.560,800,000,00 ragowar kudin albashin da aka danne.

Bayan nan an kwato ragowar kudin ma’aikatan bugi jimlar N30.280.863,588.72, an karbo ragowar N33.106.310.755.53 na alawus xin sojoji da sauran masu damara, da wasu N11,000,000,000,00 ragowar kudin tafiyar da gwamnati a kullun, da wasu N7,800,000,000,00 ragowar kudin da ake kashewa a hukumomin lafiya, wanda jimlar kudin sun kai N97.939.974,344.25.Farfesa Isah ya cigaba da cewar a shekarar 2017 kwamitinsa ta samu nasarar karbo N14,350,836,000,00 ragowar kudin da ake kashewa a hukumomin gwamnati, jimlar N3,600,000,000,00 ragowar hukumomin lafiya, da wasu ragowar kudin da ake kashewa kullun kashi na daya da suka kai jimlar N36,607,557,616,59, da wasu karin N32,394,067,541,11 na kuxaxen da ake kashewa kullun na tafiyar da gwamnati karo na biyu, haka an samo N23,508,637,038,30 wanda gaba daya kudaden sun kai jimlar N110,461,098,196,00. Yace a shekarar 2018, kwamitinsa ta karvo jimlar kudi da suka kai jimlar N387,888,899,702,16.Dan haka ba yadda kasar nan za ta cigaba dole sai mun hada hannu mun yaki rashawa ta kowace fuska wanda hakan ne zai iya tsalkake mana kasar nan.Dakta Gbongbo Ibrahim Yahaya Takuma, shi ne shugaban hukumar wayar kai ( NOA) a Neja, yace kungiyoyi masu zaman kan su da shugabanni na da rawar takawa wajen wayar da kan jama’a illar numfashin cutar rashawa wadda itace silar durkushewar tattalin arzikin kasa da na iya janyo musifu da tabarbarewar lamurra.

Da yake jawabi, gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da ya samu wakilcin kwashinan ma’aikatar sadarwa da tsare tsare, Malam Muhammadu Sani Idris, yace gwamnatin jiha na bakin kokarinta wajen baiwa hukumomin da abin ya shafa damar aiwatar da ayyukan su yadda ya kamata.

Sai dai ina kira ga jama’a da lallai su fara tsalkake kawunan su, wanda idan sun yi hakan za su zama abin koyi ga al’umma, muna bukatar yin aiki tare ta hanyar wayar da kai da anfanin gujewa yaduwar rashawa.Farfesa Etannibi Alemika, wanda mamba a kwamitin PACAC, ya gabatar da mukala inda ya janyo hankalin jama’a illar rashawa a kowace fuska, da ya shafi zamantakewa, aikin gwamnati da tafiyar tsarin addini yadda ya dace.

Farfesa Femi Odekunle, shi ne shugaban taron, ya yabawa sarakunan gargajiya da kungiyoyi masu zaman kan su wajen baiwa kwamitin goyon baya, inda ya bukaci su yi anfani da bayanan da aka yi da mukalolin da aka gabatar wajen kyautata hali da ayyuka wanda a karkashi su ne rashawa ke yaduwa.

Taron dai ya samu halartar sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaro, da manyan jami’an gwamnati da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam da masu sanya idanu akan yadda hukumomin gwamnati ke kashe kudaden gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *