Spread the love


A zaben da aka gudanar na kananan hukumomi a jihar Gombe a ranar Assabar  APC mai mulkin jihar ta lashe shugabanin kanann hukumomi 11 da kansiloli 114, a zaben da aka yi ba tare da an kai akwatunan zabe kowacce mazaba ba.


Mazabu uku ne kawai a kowanne bangaren mazabar Sanata aka kai akwati daya na Gwamna a Gombe ta arewa da mataimakin sa a Gombe ta kudu da na shugaban majalisar dokoki a Gombe ta tsakiya.

Jamaa sun fito dan neman jefa kuriu a wasu mazabun a jihar amma rashin fitar da kayan zaben ya sa suka hakura, suka koma gidajensu.


A Talata data gabata jamiyyar ta APC ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben kananan hukumomin sun fada cewa duk Najeriya jamiyya mai mulki ce take cin zabe dan haka ba za su bar wata jamiyya tama fito ba domin APC kadai ke takara a jihar.


A lokacin taron wani jigo a jamiyyar kuma shugaban kwamitin zaben Habu Mu’azu, ya kara fadin cewa a wata jiha ma akwai wata kaza da tayi kwai  guda 44 ta fafe duka babu baragurbi suma a Gombe da suke da kwai 11 su ma kazar za ta fafe duka.

 Gwamna Inuwa Yahaya, ya jefa tasa kuri’ar ne a mazaɓarsa ta cikin gari a unguwar jekadafari a sakandaren kimiyya ta gwamnatin jiha tare da wasu magoya bayansa.


Bayan kammala abun da suka kira zaɓe shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Gombe Sa’idu Shehu Awak, ne ya sanar da wadanda suka lashe zaɓen a kananan hukumomi goma sha daya kamar haka Akko Usman Abubakar Barambu, karamar hukumar Balanga Garba Umar sai Billiri Magret Bitrus, da Jamilu Ahmed Shabewa a Dukku da Ibrahim Adamu Chalu a Funakaye.


sauran sune Aliyu Usman Haruna a karamar hukumar Gombe sai Faruk Aliyu Umar a Kaltungo da Ibrahim Buba a Kwami, Musa Abubakar Nafada sai Yohanna Lahary a Shongom da kuma Shuaibu Buba Galadima a karamar hukumar Yamaltu Deba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *