Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya kalubalaci jam’iyar APC da ta bayyana gwamnan da yake bayan masu tayar da kayar bai a arewa maso yammacin Nijeriya.

Jam’iyar APC a wani bayani da ta fitar wanda mukaddashin sakataren yada labaranta Yakini Nabena ya sanywa hannu ya yi kira ga jami’an tsaro su bincike  wani gwamna da ba a bayyana sunansa ba saboda yana da hannu ga yawaitar tayar da kayar bai a yankin.

Tambuwal yana mayar da martani ya ce ba wani gwamna a kasar nan da bai yi rantsuwa a lokacin kama aiki zai kare rayukka da dukiyoyin mutanensa ba.

Ya ce akwai mamaki a yi tunanin akwai gwamnan da zai yi wasa da rantsuwar da ya yi ya kawo sabawa doka a cikin al’umma.

Tambuwal da ya yi wannan kalami ne kafin ya kilace kansa ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su gayyaci Nabena don ya fadi wannan gwamnan a yankin kuma ya fito da hujjojinsa domin taimakawa jami’an tsaro gaskiya ta yi halinta. 

Shawarata ga duk wani mai ruwa da tsaki ya sanya rayuwar mutane a gaba kafin komai ganin laifin juna ba lokacinsa ba ne a bari jami’an tsaro su yi aikinsu na samar da tsaro a daina saka siyasa a cikin harkokin tsaro, inganta harkar tsaro aikin ne da ya rataya wuyan kowa.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *