Spread the love


Daga Muhammad Awwal Umar.

Shugaban majalisar dattawa, Dakta Ahmad Lawan ya bayyana jin dadinsa da labarin sakin daruruwan daliban da aka sace a Jumma’ar da ta gabata a makarantar kimiyya ta gwamnati dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Lawan yace labarin sakin dukkan yaran da aka sace ba tare da sun sami raunuka ba, hakan zai faranta ran iyayen su da dukkan mutane masu fata na gari a Nijeriya da kasashen waje da suka girgiza da halin da yaran suka samu kansu a ciki.

Shugaban majalisar ya taya murna musamman ga iyayen yaran da suka kasance cikin halin damuwa a yayin da suke addu’ar dawowar yaran na su cikin koshin lafiya.

Sanarwar wadda Ola Awoniyi mai baiwa shugaban shawara akan aikin jarida ya sanyawa hannu yau juma’a.

Shugaban majalisar yace, ‘yan kwanakin nan da suka wuce sun zama na rashin hankali da rudani ga iyayen yaran, malaman su da dukkan mutanen kasar nan.

“Abin bakin ciki wannan tashin hankali ya tuna mana da yadda kasar mu ke cigaba da kasancewa cikin yanayin rashin tsaro kamar satan ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 da na Dapchi a 2018.

Illar faruwar wadanann laifuffukan har yau tana tare da mu, kuma mun yi zaton cewa nuna rashin jin dadin mu da Allah wadai da muka yi irin wannan abu ba zai kara faruwa ba a Nijeriya.

“Kara faruwar wannan abin bakin ciki ya ishe mu gargadi da zai sa mu samar da dukkan abin da ake bukata don samar da tsaro a makarantun mu, da ma duk wuraren da yaran mu ke taruwa don kare su daga hare-haren yan ta’adda.

“Ina mai godiya ga matakan gaggawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da sauran jama’a su ka dauka da ya kawo sakin daliban”.

Shugaban majalisar kuma ya yaba ma jami’an tsaro da ma’aikatan tattara bayanan sirri wadanda kokarin su ya kawo karshen wannan tashin hankali cikin kankanen lokaci, tare da kira a gare su da su maimaita irin hakan wajen magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *