Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar

Gwamnatin jihar Neja ta ba da umurnin rufe dukkan makarantun jihar daga yau juma’a 18 ga watan Disamba, makarantun da abin ya shafa sun hada da makarantun faramare na jiha da sakandare, da masu zaman kansu da kuma manyan makarantu masu zaman kansu.

Sanarwar dakatarwar wadda shugaban kwamitin yaki da yaduwar annobar COVID-19, Ahmed Ibrahim Matane ya sanyawa hannu, yace rufewar ya biyo bayan dawowar yaduwar annobar a fadin kasar Nijeriya.

Ahmed Matane ya bayyana cewar dawowar annobar COVID-19 karo na biyu a fadin kasar ne ya janyo rufe dukkan makarantun jihar a rana ta uku da fara samun labarin yadda annobar ke kara hauhawa.

Shugaban yace daidai ne a yi saurin dakile yaduwar a jihar ganin yadda take yaduwa kamar wutan daji, yace gwamnatin jiha ta bada umurni dukkan ma’aikatan jiha da su zauna gida daga ranar littinin 21 ga watan Disambar wannan shekarar zuwa lokacin da ba a bayyana ba, dan samun damar fuskantar wannan jan aikin da ke gaban mu.

Shugaban kwamitin wanda shi ne sakataren gwamnatin jiha, ya janyo hankalin al’ummar jihar da su gaggauta dawo da anfani da takunkumin fuska, baiwa juna tazara dan kaucewa yaduwar annobar a jiha, yace annobar ta dawo da karfi a wannan karon.

Wannan bayanin na kunshe ne a wata takardar sanarwa da jami’in yada labaran sakataren gwamnatin jiha, Malam Lawal Tanko ya rabawa manema labarai yammacin jiya Alhamis.

Ya ce duk da wayar da kan jama’a da gwamnatin jiha ta ke yi, abin mamaki ne ganin yadda jama’a ke cunkusuwa wajejen ibada, bankuna da kasuwanni, tashoshin motoci a fadin jihar.

” Za mu dauki matakai masu tsauri dan ganin ba mu bar annobar damar samun yaduwa a jihar ba, ta yadda za mu dauki matakan gaggawa wanda dole al’ummar jihar su bi wadannan dokokin”, kamar yadda Ahmed Matane ya bayyana.

Shugaban kwamitin COVID-19, ya jawo hankalin bankuna, kasuwannin zamani, da wajajen taruwar jama’a, tashoshin motoci da direbobin motoci masu zaman kan su da su bi dokokin da aka gindaya na duk wanda bai sanya takunkumin fuska ba kar su dauke shi, dan kaucewa yaduwar annobar a cikin al’umma.Shugaban ya bayyana cewar matakan da suke dauka a yanzu, na daga cikin kudurin gwamnatin jiha na kaucewa yaduwar annobar da ke kashe mutane cikin kankanin lokaci, wanda hadin kan da jama’a zasu bayar shi ne zai bada damar samun wannan nasarar dole sai an bi dokokin kare kai daga annobar COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *