Spread the loveGwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya killace kansa biyo bayan tafiye-tafiyen da ya yi a kwanakin  da Suka gabata domin ya hadu da manyan mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar Korona, hakan ya sa masana kiyon lafiya suka ba shi shawarar ya killace kansa.
“Kan haka na janye duk wata mu’amala ta aiki a zahiri har sai na kammala cika sharuddan da aka gidanya kan cutar Korona daga yau Jumu’a”.
Tambuwal a wata takarda da ya fitar aka rabawa manema labarai  ya ce ya mika ragamar jagorancin jiha ga mataimakinsa Manir Muhammad Dan’iya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ce zai bi sharuddan kwamitin kula da cutar na jihar Sakkwato da hukumar kula da cirutoci ta kasa NCDC da hukumar kula da cirutoci ta duniya(WHO) zai bari a yi masa gwaji kuma a fitar da sakamakon don jama’a su sani. Haka ma ya yi kira ga jama’ar jihar Sakkwato su bi ka’idojin kariya ga cutar, a yawaita yi masa addu’a a wannan yanayi, Allah ya yi wa mutanen Sakkwato da Nijeriya albarka.

Cutar Korona ta dawo a karo na biyu fatar da ake da ita kar ta yi kamari kamar ta farkon ganin yanda talakawa suka sha wahala a farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *