Spread the love

Matsalar tsaro dake addabar yankin arewa ya jefa fargaba da shakku a cikin al’ummar yankin abin da ya kai ga rufe makarantun kwana a jihohin Katsina da Jigawa da Zamfara da Kano da Sakkwato ta baya bayan nan kenan.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rufe makarantun kwana 16 dake kan iyaka(Boda) da jihar Sakkwato.

Wannan umarnin ya biyo bayan taron majalisar tsaro ta jiha karo 17 da aka gudanar a jiya Laraba

Kwamishinan ma’aikatar ilmi Alhaji Bello Muhammad Guiwa ne ya sanar da hakan a wata takarda da aka aikawa manema labarai, wadda mai baiwa gwamna shawara a harkokin yada labarai Muhammad Bello ya sanyawa hannu an zayyano makarantun da abin ya shafa. 

Sikandaren mata ta Illela, Sultan Muhammadu Tambari Arabic Secondary School, Illela, Gamji Girls College, Rabah, Government Secondary School, Gada, Government Secondary School, Gandi and Government Secondary School, Goronyo

Sai kuma Government Secondary School, Isa, Government Secondary School Sabon Birnin Gobir, Boarding Primary School, Isa, Boarding Primary School, Balle and Boarding Primary School, Jabo.

Sauran su ne karamar sikandare a Sabon Birni, Government Secondary School, Kebbe, Government Secondary School, Tureta, Government Technical College, Binji and Olusegun Obasanjo Technical College, Bafarawa.

Gwamnan ya ce rufewar ta wuccin gadi ce tsawon sati biyu, don ya bukaci shugabannin makarantun su bi umarnin da aka shata yanda yake. 

Bayanin yana nuna bayan sati biyu in aka samu saukin abubuwa yara za su koma makaranta a cigaba da karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *