Spread the love


Daga Muhammad M. Nasir.


Zaɓen majalisar matasa ta ƙasa reshen jihar Sakkwato yana ƙaratowa a satin nan za a gudanar da shi, ɗaya daga cikin masu neman zama shugabannin ƙungiyar Yusuf Muhammad ya bayyana dalilin da ya sa yake son shugabancin domin ganin yanda lamurran matasa suka gurgunce a jihar Sakkwato kuma yana da gudunmuwar da zai bayar don ciyar da majalisar a gaba.

Yusuf a zantawarsa da manema labarai a Laraba data gabata ya ce tabarbareawar harkokin majalisar matasa a Sakkwato ne daya daga cikin abin da ya sa ya fito, ‘ni mutum ne mai kishin matasa da yake da su a zuciya, kuma nasan in na samu dama zan yi gyara sosai, domin nafi bayar da karfi wurin bunkasa aiyukkan matasa harka ta ce kama da samar da aikin yi, karbo su daga gidan kaso matukar bashi ne silar kai su can, gyaran halin masu shaye shaye an sanni da wannan, in na samu damar zama shugaba in mutum 10 nake dauka a baya yanzu ina iya daukar nauyin mutum 20’. A cewarsa. 

Ya yabawa kwamitin zabe don shirinsu ya tabbatar za su yi adalci hakan ya sanya fahimta a tsajaninsu ‘yan takara don su zama jagorori abin koyi.

Ya ce amatsayinsa da yake jagorantar gidauniyar Mustafa wadda ta daga darajar matasa a kalla 400 zai samu hadin kai da kungiyoyin sa kai da masu kudin da ke tallafawa matasa don a Kara kawo cigaban matasa a rage dogaro da gwamnati a wurin gudanar da shiraruwan Matasa. 

“duk wanda yake da kishin jiha ba zai shigo mana da bambancin jam’iyar siyasa ba don cigaban Sakkwato aka sa a gaba don an fara ganin jagoranci ya canja yanda aka gayyato kowa a wurin muhawara abin da ba a taba yi ba Gwamna Tambuwal ya yi hakan don ya baiwa matasa jagorancin al’amurransu da kansu ina fatan samun karin cigaba.” a cewar Yusuf Muhammad. 

Ya ce zai yi aiki tare da jami’an gwamnati a matayinsa na wanda yake karƙashin kwamishina ba abu ne da zai yi shi kaɗai ba, za a riƙa zaunawa a kawo shawara don tafiya tare cikin cigaba domin dai matasan ne a zuciya.

“ina da burin samar da shiri da za mu haɗa da ma’aikatar ilmi don ganin an tallafawa matasa da ba su son makaranta amma suna da basira ta wani abu kamar ƙwallo, ba wai ƙyale si za a ƴi ba za a tabbatar basirarsu ta yi amfani, na shirya yanda zan ciyar da matasa sosai kafin na fito takara.” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka yana kan fito da wata manhaja a yanar gizo domin ɗaukar bayanan matasan Sakkwato waɗanda suka yi karatu da waɗanda ba su yi ba don ganin abin da za a iya yi masu na taimako a dai samu cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *