Spread the love

Jaruma a masana’antar shirya finafinan Hausa Fati Abdullahi wadda aka fi sani da Washa, ta yi fice a farfajiyar wasan Hausa amma an daina jin ɗuriyarta a kwanan nan.

Jarumar ta yi fice a harkar wasan Hausa kuma ta ja zarenta yanda take so a kwanan dai ne aka daina ganin fuskarta a finafinnai masu dogon zango da aka soma a yanzu da waɗanda aka saba da su masu gajeren zango.

Masoyan Fati Washa sun riƙa tambayar ina ta shige ne abin da ya sanya Managarciya neman sanin halin da take ciki kenan.

A bayanin da waƙilinmu ya samu Fati tana nan lafiya ƙalau hasalima yawan harkokinta da take yi ba wanda ya samu cikas kuma ba ta bar harkokin fim ba tana yi a kwanannan ma fim ɗinta zai shiga kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *