Spread the love


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

A wani mataki na yaƙi da yaɗuwar COVID-19 waton korona a jihar Neja, Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ne ya umarci ma’aikatan jihar da kowa ya zauna a gida daga ranar littinin 21 ga watan Disamban 2020.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da gwamnatin jihar ta raba wa ma’aikatunta a yau alhamis wadda ta sami sa hannun shugabar ma’aikatan jihar, Malama Salamatu Abubakar.

Sanarwar ta nuna cewa, gwamnatin jihar ta ɗauki wannan mataki ne duba da dawowar annobar COVID-19 karo na biyu a ƙasa.

An bukaci kananan ma’aikatan su zauna a gida har sai baba ta gani.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Cibiyar yaƙi da yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bada sanarwar samun ƙarin mutum 930 da suka kamu da cutar a tsakanin sa’o’i ashirin da hudu da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *