Spread the love


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

“Ina taya shugaban kasa, mai girma Muhammadu Buhari murna a yayin da yake murna cika shekaru 78 da haihuwarsa a ranar Alhamis.

“Ina hade da dangi, abokai, jami’an gwamnati da abokan hulda na shugaban kasa wajen taya shi murna yin bikin wannan rana cikin koshin lafiya da karsashi.”

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin bayanan da shugaban ya sanyawa hannu, aka akewa kafofin yada labarai kan cikar shugaban kasa shekaru 78 da haihuwa.

Takardar sanarwar ta cigaba da cewar, a duk shekarun da shugaba Buhari yayi a shugabancin kasar nan ya nuna cikakkiyar jajircewar sa akan samar da hadin kai, zaman lafiya da cigaban Nijeriya.

Tun daga samar da abubuwan more rayuwa a duk fadin kasar nan, shirye-shirye na musamman da aka tsara don taimaka ma masu karamin karfi ya zuwa tsare-tsare don rarraba hanyoyin tattalin arzikin, shugaba Buhari yana amfani da gaskiyarsa da kimarsa a idon talaka Nijeriya, dan fidda ta daga cikin yanayi mai wahala zuwa kasa mai inganci da walwala.

Ya cigaba da cewar ina kira ga dukkan yan kasa su fadada tunanin su da hangen gaba, su cigaba da tsayawa kafada da kafada da shugaban kasa a wannan aiki na kishin kasa.

A matsayi na na dan jama’iyar APC, ina mai farin ciki da yadda shugaba Buhari ya sa aniya ta gyara da sake gina kasaitarciyar jama’iyar mu don ta cimma burinta na shugabantar Nijeriya zuwa ga cigaban siyasa da tattalin arziki.

A bangaren mu, majalisar dokoki ta tarayya za ta cigaba da aiki cikin kwanciyar hankali da shugaban kasa domin cin ma zaman lafiya da cigaban Nijeriya da cigaban mutanen mu.

A wannan rana mai muhimmanci na zagoyar ranar haihuwar sa, ina addu’a ga Allah madaukakin sarki yaci gaba da ba shi fasaha, karfin gwiwa da lafiya don samun cigaba da shugabancin kasar nan da zai kai mu ga inda yan kasa ke bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *