Wani matashi a garin Yola Jihar Adamawa a arewacin Nijeriya yabi Sahun Suleman Panshekara Wajen Auren Wata Baturiya ‘yar ƙasar Amerika.

Angon ya zo da amarya saman babur mai ƙafa uku wanda ake kira adaidaita wurin buki abin da ya ƙara jan hankalin mutane kan yadda ya ɗauko amaryar a babur a yankin da ba a ɗaukar amarya sai a cikin mota ta alfarma.

Da fatan Allah Ya ba su zaman Lafiya, wannan ne karo na biyu da wani matashi ya auri mace Baturiya a arewacin Nijeriya.

Managarciya ta samu labarin da yawa wasu Hausawa na aure a ƙasashen turai sai dai a can ne ake yin komai, saɓanin waɗan nan da suka yi anan.

Auren Baturiya an mayar da shi wata canyewa da birgewa a tsakanin Hausawa har wasu na ganin kamar yin hakan wani abu ne na musamman.

Wasu sun ɗauki auren so ne da ƙauna ya sanya don haka ba wani abun talla ba ne don kowa yana aure da wadda yake muradi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *