Daga Babangida Bisallah.

Majalisar dattawa zata yi zama na musamman a ranar litinin mai zuwa don amincewa da kasafin kudin badi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

Shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya bada sanarwar hakan a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
Shugaban majalisar ya ce an samu tsaiko na wajen amincewa da kasafin kudin domin ba kwamitin majalisar akan kasafin kudi damar shigar da sabuwar bukatar bangaren zartarwa na karin kudaden da za a kashe.


Ya ce kwamitin na aiki dare da rana, kuma ya shirya mika rahoton sa a yau amma an samu sabuwar bukata ta karin kudaden da za a kashe gab da hada rahoton daga bangaren zartarwa a don haka aka dage mika rahoton saboda a samu yin aiki mai kyau akan kasafin kudin.
Yace kwamitin ya tabbatar da za a gama aiki akan rahoton a karshen makon nan don haka majalisar zata yi zama na musamman ranar Litinin, 21 ga watan Disamba don kawai amincewa da kasafin kudin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *