Spread the love

Gwamnan Kano Dakta Umar Abdullahi Ganduje a jiya Alhamis ya faɗi daliƙinsa na cire Sarkin Kano Muhammad Sanusi daga karaga.

Gwamnan ya ce yi yi haka ne domin ya tseratar da masarautar ga zagi.

Ya yi waɗannan kalamai ne a wurin ƙaddamar da littafin Jonathan da wani ɗan jarida Philips Melah ya rubuta a cewasa a lokacin da aka naɗa Sanusi 2014 ba shi ne yafi cancanta ba an yi ne don kawo tangarɗa ga Jonathan.

Jonathan ya sallami tsohon Sarki a matsayin gwamnan banki ne bayan da ya fallasa ɓacewar kuɗi dalar Amerika biliyan 49 a cikin gwamnatin Jonathan.

Ganduje ya ce a lokacin da na zama gwamna na fahimci maganin da Jonathan ya yi amfani da shi a biyan buƙata ga cutar da ta dame shi nima irinsa yakamata na yi amfani ga marar lafiyana.

“Na yi amfani da maganin Jonathan domin na tseratar da masarauta da tsarin, na ko yi hakan daidai, ni da Jonathan muna tare ba za mu yi dana sani ba kan matakin da muka zartar” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *