Spread the love

Gwamnatin Nijeriya ta umarci kamfanonin sadarwa dake kasauwanci a ƙasar su karɓo nambobin shedar zama ɗan ƙasa(NINs) wurin abokan hulɗarsu nan da sati biyu.

Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin a lokacin da ya yi taro da shugabannin hukomin dake ƙarƙashin ma’aikatarsa, hukumar sadarwa ce ta fitar da bayanin a daren jiya Talata.

Daga jiya an ba su sati biyu 16 ga disamba zuwa 30 duk layin da ba a haɗa bayanansa da nambar ba za a rufe shi.

Minista da sauran shugabanni za subtabbatar kamfanonin layukkan waya sun bi dokar, duk kamfanin da ya ƙi bin umarnin za a karɓe lasisin gudanarwarsa a Nijeriya.

Gwamnati ta yi kira ga mutane su tabbatar da an sanya nambarsu a wurin bayanan rijistarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *