Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.


Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ba da tabbacin jihar sa za ta zama sahun gaba a noman shinkafa a kasar nan.

Gwamnan ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman shinkafa ta rani a filin kasuwar baje koli dake minna, wanda babban bakin Najeriya da hadin guiwar manoman shinkafa ta Najeriya ( RIFAN) suka shirya a Minna.

Gwamnan ya bayyana cewar taron ya nuna irin kwazo da jajircewar da manoman shinkafa suka nuna a jihar, yace wannan na daga cikin kudurin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na karfafa guiwar manoma dan samar da abinci a kasar nan.

Ya bayyana cewar jihar Neja a hankali za ta wadatar da kasar nan da sauran kasashe da abinci musamman a bangaren noman shinkafa.

Gwamnan yace jihar Neja na da wadataccen kasar noma, wanda zai cigaba da ba da damar noman shinkafa wanda ta ke bukatar goyon bayan gwamnatin tarayya a noman shinkafa a jihar.

Ya karfafa guiwar manoman jihar da su kara mayar da hankali musamman ga noman rani, musamman ganin manoma da dama sun yi hasarar anfani gona sakamakon anbaliyar ruwan sama na wannan shekarar.

Yace gwamnatinsa za ta cigaba da baiwa bangaren noma muhimmanci dan samar da wadataccen abinci da samar da ayyuka ga jama’ar jihar.

Dan haka gwamnati za ta cigaba da yin hadin guiwa da RIFAN dan karfafa guiwar manoman shinkafa, rogo da masara da sauran nau’ukan abinci a jihar da kasa baki daya.

Ya bayyana kudurin gwamnatinsa na inganta bangaren noma ta hanyar karfafa guiwar manoman kwakwa dan samar da manja wanda yana daya daga cikin abinda ake bukata a kasar nan.A bayaninsa, gwamnan CBN, Mista Godwin Emefele yace kaddamar da shirin na daga cikin yunkurin gwamnatin tarayya na karfafa guiwar manoma ta hanyar noman shinkafa a kasar nan.Gwamnan babban bankin wanda ya samu wakilcin Mista Edward Lametek Adamu, yace gwamnan CBN yace shirin bada tallafi ga manoma wanda gwamnatin tarayya ta kirkiro zai taimaka wajen baiwa kananan manoma kwarin guiwar samun kudaden yin noma ta hanyar bunkasa cimaka a kasar nan, wanda zai baiwa tattalin arzikin kasa damar samun bunkasa da kirkiro ayyuka ga kasa.

Yace yin hadin guiwa da RIFAN zai baiwa bangaren noma samun cin gashin kai musamman wajen bunkasa bangaren noma a kasar nan.

CBN tace biyan tallafin daga hannun wadanda suka ci gajiyarta, dan haka akwai bukatar RIFAN ta kara kaimi wajen ganin manoman da suka samu bashin sun mayar da kudaden kamar yadda aka tsara dan cigaba da baiwa CBN kwarin guiwar cigaba da bada bashin noma ga manoma.

Daga cikin mahalarta taron sun hada da shugaban RIFAN ta kasa, Alhaji Aminu Muhammad Goronyo, wanda ya bayyana cewar RIFAN za ta samar da ton miliyan goma na shinkafa a noman rani a kasar nan, Alhaji Idris Usman, kodinetan RIFAN/CBN a Neja, yace gwamnatin jihar ta bada gudunmawa sosai a bangaren noma, dan haka ya jawo hankalin CBN da ta gaggauta bada kayan gona kan lokaci domin manoma kusan sun fara makara da wata daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *