Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Daya daga cikin ‘yan takarar shugaban majalisar matasa na jihar Sakkwato Sanusi Sarki ya yi alkawalin matukar ya samu nasarar zama shugaban majalisar zai yi aiki tukuru ta yadda zai sauya abubuwa a majalisar domin kawo cigaban matasa da jihar.

Dan takarar a zantawarsa da Managarciya a satin da ya gabata ya ce “zan samar da majalisar matasa sabuwa hul da ba a taba irinta ba a Sakkwato, basira ta dana samu a baya dana yi mataimakin shugaban majalisa na halarci tarukka da dama da suka shafi matasa zan yi amfani ita ganin yanda muka samu gwamnan matasa da kwamishina da mai baiwa gwamna shawara duk matasa ne masu kishin cigabansu.” A cewarsa

Sanusi Sarki ya bayyana cewa nasarorin da suka samu a wurin hada kai da gwamnati don samar da cigaban matasa da aiki tare a tsakanin matasa ba nuna bambancin siyasa manufa kawai a kawo shiraruwa matasa su amfana ba sai an cigaba da jiran gwamnati ba.

“Za mu fito da hanyoyin wayar da kan mutane su rika shiga shiraruwan amfani, da kara karfafa burin gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal na kawar da bangar siyasa da roke-roke a ma’aikatun gwamnati hakan na cikin ginshikan da muka sa a gaba.

“Majalisa tana da wuraren da take samun kudi za mu kara karfafa su don kara rike majalisa, da cigaba da wayar da kan jama’a illar shaye-shaye da aiyukkan barna.” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *