Spread the love

Daga Babangida Bisallah

Gwamnatin Neja za ta yi hadin guiwa da Lee Group ta kasashen waje dan bunkasa harkar noma, kasuwanci da hakar ma’adinai a Neja.

Kamfanin yanzu haka ta nemi hekta talatin na fadin kasa a Suleja saboda kudurinta na kafa matsugunnin kasuwanci dan ajiye motoci da sauran kasuwanci.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya jagoranci zaman taron da sauran mukarraban gwamnati da kamfanin inda ya amince wa kamfanin da ya zuba jari a jihar.

Gwamnan ya baiwa ‘yan kasuwar masu bukatar zuba jari a jihar tabbacin cewar, gwamnatinsa a shirye ta ke da ta samar wa masu zuba jarin wajen da zasu yi anfani da shi dan bunkasa tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.

Ya bayyana cewar yana bukatar samun nasarar Lee Group wanda zai baiwa sauran masu zuba jari sha’awar shigowa jihar dan yin hadin guiwa.

Lee Group kamfani ce da ke muradin yin abubuwa da dama dan anfanin kasa, ta kowace fuska.

Kamfanin yana gudanar da kasuwanci a bangarori da dama a Najeriya tun shekarar 1962.

Kwamishinan kasuwanci, Dakta Mustapha Jibrin da kwamishinan shari’a, Barista Nasara Danmallam na daga cikin manyan jami’an gwamnati da wasu manyan mukarraban ma’aikatar kasuwanci da suka halarci zaman taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *