Spread the love


Daga Babangida Bisallah.

Duk da yunkurin gwamnatin jihar Neja ta yi ba a samu daidaito ba kan janye yajin aikin ma’aikata da kungiyar kwadago ke jagoranta, kungiyar ta jaddada matsayinta na kin janye yajin aikin.

A wata takardar manema labarai da kungiyar ta fitar ta bayyana cewar dole sai an warware matsalolin da ake takaddama tsakaninta da gwamnati da ya shafi albashin ma’aikatan jihar da na kananan hukumomin jihar.

Tunda farko dai kungiyar ta bukaci gwamnati ta gaggauta biyan kashi talatin da ta cire na ma’aikatan jiha, wanda zuwa yanzu wasu ma’aikatan sun tabbatar da gwamnati ta mayar da kudaden da gwamnatin ta zaftare masu.

Amma Kungiyar ta cigaba da cewar akwai kashi talatin na albashin ma’aikatan kananan hukumomi da aka zaftare kuma har yanzu ba a biya ba.

Takardar ta kara da cewar akwai ma’aikatan jiha su a kalla 80 da aka kora aiki da har yanzu ba su san matsayinsu ba, bayan nan akwai maganar kudin hutu da wasu kudaden da ya kamata a ce ma’aikata na anfana da kusan gwamnati tayi watsi da su.

Zuwa yanzu jama’a na ji a jikinsu sakamakon tsayawar wasu muhimman abubuwa na rayuwa musamman ruwan sha da ma’aikatan ruwa suka tsunduma yajin aiki, da marasa lafiya da ke kwance a asibitocin gwamnati da zuwa yanzu sun rasa malaman jinya da za su duba su.

Kungiyar NLC dai ta dora ayar tambaya ga gwamnatin jiha da shugabanin kananan hukumomi kan yadda suke kashe kudaden shiga da ke aljihun su da ya kasa wadatar da su, da har sai sun taba albashin ma’aikatan jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *