Spread the love

Daga Babangida Bisallah

A yunkurin bunkasa bangaren noma a Neja, sakataren gwamnatin jiha, Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana cewar gwamnatin jiha ta bayyana kudurinta na tallafawa kananan manoman a dukkan fadin jihar duk da barazanar cutar korona da ya addabi duniya.

Matane ya bayyana hakan a bukin girbe anfanin gona a Abuja, wanda gidan radio Zuma 88.5 FM ta shirya, wanda aka yiwa lakabi da anfani da gidajen radio kan tsaron abinci da harkar noma a Najeriya.

Sakataren wanda shi ne shugaban kwamitin kula cutar COVID-19 a jihar, yace  hakkin gwamnatin jiha ta goyi harkar noma a dukkanin fadin jiha duk da barazanar yaduwar cutar COVID-19.

Ya cigaba da cewar, gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello ta shirya wadata bangaren harkar noma dan samun bunkasar abinci dan samar da tsayayyun manoma, dan haka za mu cigaba da baiwa bangaren noma muhimmanci.

A cewarsa, “gwamnati za ta cigaba da karfafa guiwar jama’a musamman dan baiwa matasa kwarin guiwa akan harkar noma domin samun dogaro da kai”.

Da ta ke bayani a taron, uwargidan gwamnan Neja, Dakta Amina Abubakar Sani Bello, da ta samu wakikcin kwamishina ruwa, Alhaji Yusuf Sulaiman, tace gwamnatin jiha ta himmantu wajen karfafa guiwar manoma a karkashin shirin tallafin kananan manoma domin samar da gurabun ayyuka ga matasan jihar.

Da yake bayani bayan kammala taron bukin, a gidan radio Zuma 88.5 FM na kai tsaye, ya jawo hankalin al’ummar jihar da su cigaba da bin dokokin da aka gindaya wajen kaucewa kamuwa da cutar COVID-19, ta hanyar yawaitan wanke hannu, cigaba da bada tazara tsakanin juna, duk wanda ke atishawa ya kaucewa taba hancinsa, idanu da baki da hannunsa, tare da kaucewa yaduwar cutar a cikin jama’a.

Inda ya bayyana cewar cutar COVID-19 gaskiya ce, ba cuta ce mutanen ketare ba ne ta kan shafi duk wanda bai kiyaye ba, dan haka ya kamata duk wanda ke da alamunta a jikin shi ya guji shiga cikin jama’a.

Taron karo na hudu, wanda an shirya shi ne dan cikar gidan radio shekaru goma sha biyar da kafuwa, ya samu halartar, shugaban majalisar dokokin Neja, Honarabul Abdullahi Bawa Wuse, da kwamishinan sadarwa da tsare-tsaren kafafen yada labarai, Hon. Muhammad Sani Idris, da kwamishinan manyan makarantu, Farfesa Baba Ali, da wasu manyan jami’an gwamnatin jiha.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *