Spread the love


Daga Babangida Bisallah.

Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Suleja, Tafa da Gurara Honarabul Abubakar Lado ( Mai ALLAH) ya kai tallafin kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar karamar hukumar Shiroro da mahara suka daidata.

Dan majalisar ya jajanta wa ‘yan gudun hijirar, inda ya bayyana cewar hare-haren maharan ga mutanen karkara abin takaici ne da Allah waddai, inda ya nemi gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen dakile ayyukan batagarin.

Ya jawo hankalin maharan da su dauka wannan abin da ya same su wata kaddara ce daga Allah, kuma su kara kaimi wajen addu’o’in kawo karshen ayyukan batagarin.

Daga cikin kayayyakin da ya baiwa ‘yan gudun hijirar sun hada da wake, shinkafa, taliya da indomie da sabulan wanka dana wanki.

Haka kuma ya bada man shafawa da takalmin yara, bargunan rufa da tabarmi, inda ya bayyana cewar yanzu haka ya kammala shiryawa da kwararrun likitoci dan zuwa duba yara saboda sanyin da ake fama da shi dan gudun kamuwa da cututtuka.

Da yake karban kayan tallafi a madadin ‘yan gudun hijirar, shugaban karamar hukumar Shiroro, Honarabul Sulaiman Chukuba, ya yabawa dan majalisar, bisa tausayawa da ya yiwa wadannan al’ummomin, inda ya bayyana cewar zai tabbatar kowa ya samu tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *