Ma’aikata sun shiga yajin aiki tare da gudanar da addu’o’i kan zaftare masu albashi da gwamnatin Neja ta yi


Daga Babangida Bisallah, Minna.


Kungiyar kwadago ta NLC da TUC sun gudanar da addu’o’in kan rage albashin ma’aikata a jihar Neja da aka yi.

Shirin na daga cikin kudurin kungiyar bayan shiga yajin aikin a rana ta biyu wanda aka fara shi jiya laraba a dukkanin fadin jihar.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a harabar sakatariyar NLC da ke Minna, shugaban NLC na jihar, Kwamared Yakubu Garba, ya ce yanzu haka tun jiya suka umurci kananan hukumomi su gudanar da addu’o’in a yankunan kananan hukumomin su, duba da yadda gwamnatin jihar ta ke zaftare albashin ma’aikata ba tare da wani dalilin ba.

Ya cigaba da cewar a watan Disambar 2019 gwamnatin ta zaftare kashi talatin cikin dari na ma’aikatan kananan hukumomi wanda har yanzu ba a mayar ba, watan Nuwambar da ta wuce na wannan shekarar haka ya faru da ma’aikatan jiha, wanda muna cikin da jami’an kwamitin gwamnati ba mu kammala wannan zaman ba, sai kawai muka ga su ma ma’aikatan jiha haka ta same su.

Dan haka mun taru dan kai koken mu ga Allah akan wannan karfakarfar da ake mana da hakkin mu, muna kan yajin aikin sai baba ta gani, haka kuma za mu cigaba da yin addu’o’in, duk wanda ke da hannu akan wannan lamarin Allah yai mana maganin sa.

Kwamred Tanimu Kagara, shi ne shugaban kungiyar TUC ta jiha, yace muna goyon bayan ma’aikatan jiha akan wannan kudurin, dan bai kamata a cigaba da yiwa ma’aikaci yadda ake so ba, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Abin da ya shafi ma’aikacin jiha, ya shafi na karamar hukuma, NULGE na cikin wannan tafiyar, dan haka za mu hada hannu wajen gwagwarmayar bin hakkin ma’aikata.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *