Spread the love


Daga Babangida Bisallah, Minna.

Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin cafke masu saran itace a daji da masu kona gawayi ba bisa ka’ida ba, shugaban kwamitin kula da saran itatuwan daji da kona itace dan yin gawayi, Malam Isah Lakpene ne ya bayyana hakan a minna lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa.

Lakpene ya cigaba da cewar sare itace ba tare da izinin hukumomin da abin ya shafa babban laifi ne, dan haka gwamnati ba za ta cigaba da zura idanu dan biyan bukatar wasu ba, alhalin haka a na janyo mata hasara mai yawa.

Ya ce akwai nau’ukan itacen da gaba daya gwamnati ba ta yarda a sare su ba, duk motar itacen da aka kama da irin wadannan nau’ukan itacen tabbas za a kwace itacen gaba daya, yanzu an kafa kotun tafi da gidanka wanda duk aka samu da laifi za a gurfanar da shi nan take, dan fuskantar hukuncin da ya dace da shi.

“Yanzu haka kwamitina ta kama motoci sama da dari biyu na gawayi wanda duk suna hannun mu, muna aiki ba dare ba rana dan sanya idanu akan masu kokarin yiwa gwamnati karan tsaye kan wannan dokar.

“Ina jawo hankalin masu baiwa jami’an mu kudade da sunan cin hanci da su sani cewar duk wanda ya baiwa wani jami’in mu kudi tamkar kyauta ce dan in yazo hannu ba za mu saurara ma shi ba.

“Masu martaba Etsu-Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ( Bagadozgi) da mai martaba Etsu-Lapai, Alhaji Umar Bago II sun yabawa wannan aikin da muke yi kuma suna kara mana kwarin guiwar cigaba da aikin nan ganin yadda hamada da ambaliyar ruwa ke kokarin lalata mana kasa sanadiyar sare itace a cikin dazukan yankin Neja ta kudu.” a cewarsa.

Lakpene ya kara jaddada cewar duk magidancin da ya ajiye buhun gawayi sama da biyar a gidansa muddin suka gan shi sai sun kame su, lokaci yayi da jama’a zasu sanya idanu dan ganin ba cigaba da yin barna ta hanyar saran itatuwa a cikin daji ba.

“Duk wanda ke son sare itacce bisa wani dalili na tilas to ya rubutowa hukumomin da abin ya shafa za su duba dan bada shawarar da ta dace.” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *