Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya ba da tabbacin cewa aikin filin jirgin saman dakon kaya na kasa da kasa na jihar Zamfara wanda gwamnatinsa ta fara zai fara aiki a watan Yunin shekara mai zuwa.

Matawalle ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Talata lokacin da ya ziyarci inda ake gudanar da aikin filin jirgin saman don duba ayyukan da ake yi a filin jirgin saman kasa da kasa na Jihar Zamfara inda ya ba da umarnin fara jigilar filin jirgin zuwa watan Yunin badi.

Gwamnan ya kuma umarci kamfanin da ke gudanar da aikin da ya tabbatar da cewa titin saukar jiragen, duk sassan tashar sun fara aiki kafin watan Yunin shekara mai zuwa, yana mai bayar da tabbacin cewa dukkan kayayyakin filin jirgin saman da kayayyakin aikin za su kasance a kasa kafin lokacin.

Matawalle ya ce Gwamnatin Jiha za ta gina sansanin alhazai na zamani na mahajjata a kusa da filin jirgin sama don saukar da maniyyatan jihar da makwabta, yayin jiran tashin su zuwa Saudiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *