Spread the love


Daga Muhammad M. Nasir


An bayyana Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wani ginshiki a jagororin siyasar Arewa da Najeriya baki ɗaya, ta la’akari da irin gudummuwar da ya bayar na ciyar da ƙasa gaba tun zamanin da yake matsayin shugaban majalisar wakilai ta Nijeriya  har  zuwa kasancewarshi Gwamna a Jihar Sokoto.


Shugaban kungiyar magoya bayan Tambuwal na Najeriya wadda a turance ake kira da suna Tambuwal Save Nageria Alhaji MD Yusuf ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a garin Kaduna.


MD Yusuf ya cigaba da cewar ayyukan ciyar da ƙasa gaba da mai girma gwamna Aminu Tambuwal ya yi, sun samo asali ne tun a shekarar 2003 lokacin da ya je majalisar dokoki ta tarayya, ya kuma rike matsayi na shugabantar kwamitoci da dama a majalisar wanda aka samu nasarori da dama, har ya zuwa shekarar 2011 zuwa 2015 lokacin da ya riƙe muƙamin Shugaban majalisar dokokin tarayya, kuma tun daga wannan lokaci har ya zuwa yanzu da yake a matsayin gwamna, kullum nasarori ya ke samu ta fuskar ciyar da ƙasa gaba.


“Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya shiga cikin jerin fitattun mutane wadanda suka samu babbar lambar yabo na manyan Gidajen Talabijin na Najeriya a matsayin waɗanda suka bada gudunmuwa na ciyar jama’ar su gaba, inda ya zama zakaran gwajin dafi kuma tauraro a tsakanin sauran gwamnonin Jihohin ƙasar su 36”.

Ga mutane da yawa, kyakkyawan shugabancin Gwamna Tambuwal ne ya tabbatar masa da samun wannan babbar lambar yabon da ma wasun su masu yawa da ke tafe.”Ku bani dama na bayyana maku wasu daga cikin namijin kokarin da suka cancantar da Gwamna Tambuwal samun wannan babbar lambar yabon a yau din nan”.


MD Yusuf ya cigaba da cewar “Hawansa kujerar mulki ta Gwamnan Jihar Sakkwato na shida, an fara fahimtar irin sauyin juyin-juya-halin da ya zo da shi ne musamman a fannin Ilimi na Jihar Sakkwato, a lokacin da ya baiwa sashen na Ilimi mahimmanci a cikin kasafin kudinsa”. 


Kason da Gwamna Tambuwal ya ware wa fannin Ilimi na baya-bayan nan shi ne, Naira Bilyan 47, 880, 096, 366 .25, wanda hakan ke daidai da kashi 24% na jimillan kasafin kudin Jihar ta Sakkwato na Naira Bilyan 202, 444, 458, 429.02, tabbas wannan kyakkyawar shaida ce”.


MD Yusuf ya ƙara da cewar “Duk domin dai kara karfafa wa sashen na Ilimi, an kafa tare da kaddamar da wata gidauniyar bunkasa Ilimi ta musamman a karkashin shugabancin Mai Martaba, Sarkin Musulmi, Dakta Muhammadu Sa’ad Abubakar III, Sultan na Sakkwato. Wannan gidauniya wacce aka tabbatar da cewa ita ce irin ta ta farko a tarihin Jihar Sakkwato, ta bayar da damar bayar da gudummawar daidaiku ne domin bunkasa sashen na Ilimi”.


Amma kamar yanda masu iya Magana suke cewa ne, ‘tafiyar shekaru dubu, ana fara ta ne da takon kafa guda,’ namijin yunkurin da Gwamna Tambuwal ya fito da shi, a yanzun haka ya fara haifar da da mai ido. Daya daga cikin kyakkyawan sakamakon da yunkurin na Gwamna Tambuwal ya fara samarwa shi ne yanda a yanzun haka yaran da a baya sam ba sa zuwa makaranta, a yanzun haka sai tururuwa suke suna zuwa makarantun, kamar yanda hukumar majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF ta bayar da shaidar hakan, inji MD Yusuf.


A maganar nan da muke yi a halin yanzun, Jihar Sakkwato ce Jiha ta farko da ta fara biyan iyaye matan da suka kai ‘ya’yansu yara mata makarantun Firamare alawus, wannan domin dai kara karfafa wa Ilimin yara mata.


Gwamna Tambuwal ya yi imani da cewa ba ta yadda za a sami nasarar bunkasa sha’anin Ilimi a Jihar ba tare da karfafan iyayen yaran da su nemi ilimi mai zurfi ba. A cikin hikimarsa, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, sai ya fahimci wajibcin baiwa hukumar bayar da tallafin karatu ta Skolashif mahimmanci. Ya zuwa yanzun, tabbace yake a karkashin Gwamna Tambuwal an kashe tsabar Naira Bilyan 7.5 domin bayar da tallafin karatu a hanyoyin Skolashif din daban-daban.


MD Yusuf ya cigaba da cewar “Gina asibitin koyarwa na jami’ar jihar Sakkwato da kuma makarantar sakandaren ilimin mata ta gwamnati a garin Kasarawa, wani yanki da ke wajen Sakkwato, ya sake sabunta harkokin kasuwanci a yankin”


“Gwamna Aminu Tambuwal ya ba da kwangilar Naira biliyan 9.2 ga wani kamfani na asali a watan Yuli, tare da kammalawar watanni 30.


An ga daruruwan ma’aikata a wurin a ranar Litinin a yayin rangadin dubawa da mambobin majalisar jihar na kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, karkashin jagorancin shugaban, Malam Isa Shuni”.


MD Yusuf ya ce kimanin ma’aikata 1000 wadanda ba su da kwarewa wadanda ke gudanar da ayyukan an samo su ne a cikin jihar ta Sakkwato, yayin da kayan aikin gini kuma aka samo su daga jihar da kuma makwabtan jihohin Zamfara da Kebbi.
Ya ce za a gina manyan asibitoci shida, dakunan gwaje-gwaje, dakuna, tsarin ruwa da hanyoyin sadarwa a wurin asibitin koyarwa.


A Kwalejin Kimiyyar ‘Yan Mata, Shugaban Ƙungiyar Tambuwal Save Nageria ya ce aiki yana gudana ba tare da matsala ba abin gwanin ban sha’awa.


“Majalisar zartarwar jihar ta amince da gina asibitin koyarwa a kan kudi Naira biliyan 6.8, yayin da makarantar za ta ci N2.4 biliyan”.


MD Yusuf ya bayyana cewar Sauran kwangilolin da aka bayar sune gina asibitoci biyu a karamar hukumar Tambuwal ta jihar akan kudi naira biliyan 1.8 da kuma wani a Sabon Birni akan kudi naira biliyan 1.7.
Shugaban Kungiyar na Tambuwal Save Nageria MD Yusuf ya lissafo wasu muhimman ayyuka da gwamna Aminu Tambuwal ya aiwatar a Jihar Sokoto


1, Aikin Babban Titin Mai Tuta Road
2, Unguwar Rogo To Gagi Randa Bawul
3, Gangaren Tashar Illelah Road
4, Sokoto State Teaching Hospital Kasarawa
5,  Makarantar ‘Yan Mata ta Government Girls Science Academy Kasarawa
6, Aikin Ginin Manyan Asibitocin Ƙwararru A Shiyyoyi Uku Na Mazaɓar ‘Yan Majalisar Dattawa
7, Sai kuma Ginin Babban filin Wasanni Stadium
8, Sai Ginin Manyan Makarantun Kwana Na Zamani
9, Sai Gudanar Da Aikin Babban Titin Koko
10, Da Babban Titin Guiwa Aka Road
11, Sai Ginin Babbar Cibiyar Lafiya Da Ke Farfaru
12, Sai Babban Dakin Taro Da ke Kasarawa
13, Sai Kwalejin Koyar Da Aikin Unguwar Zoma Dake Tambuwal
14, Sau Kwalejin Horas Da Dakarun Sojin Saman Najeriya Dake Shagari
15, Samar da Gyaran Hanyar ruwa na Mabera wanda cikin ‘yan makwanni da fara aikin, an yi nasarar kammala kaso 33 ciki 100.
16, Sai Ayyukan Samar Da Ruwa A Kananan Hukumomi 23
17, Da Samar Da Hekta 4500 Yankin Karamar Hukumar Kware
18, Gyaran Hanyar Salame Junction A Yankin Karamar Hukumar Gwadabawa
19, Aikin Titin Bypass Na Garin  Tambuwal
20, Sayar Da Gidaje Masu Saukin Kudi Ga Jama’a
21: Samar Da Hekta Kadada 4500 Don Noman rani da Damina a yankin ƙaramar Hukumar Kware.
22- Da Ayyukan tagwayen hanyoyin da aka sanya gaba ana yi yanzu haka a yankin Ruwan ɗorawa da sauran su.
23- Sannan ɓangaren matsalar rashin tsaro, Gwamna Tambuwal ya yi matukar kokari ta wannan fanni da daƙile matsalar ‘yan Bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin jihar.


Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya shiga cikin jerin fitattun mutane wadanda suka samu babbar lambar yabo na manyan Gidajen Talabijin na Najeriya a matsayin waɗanda suka bada gudunmuwa na ciyar jama’ar su gaba, inda ya zama zakaran gwajin dafi kuma tauraro a tsakanin sauran gwamnonin Jihohin ƙasar su 36.


Sauran wadanda suka samu irin wannan lambar girmawa daga manyan Gidajen Talabijin din sun hada da hamshakin dan kasuwan nan, Aliko Dangote, Gwamna Nyesom Wike, Marigayiya Farfesa Dora Akunyili, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, da Dakta Mike Adenuga, da dai sauran zaratan ‘yan Nijeriya da suka aikata wa kasar nan da al’ummar kasar nan abin alheri da su ma suka amshi wannan lambar yabon.


Bisa ga wadannan kyawawan nasarori da ya samu ya sanya jama’ar Jihar Sokoto da sauran ‘yan Najeriya Maza da Mata ke kira gareshi da ya amince ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a shekarar 2023 domin kai Najeriya ga tudun mun tsira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *