Spread the love

 


Daga Muhammad M. Nasir.


Gidauniyar Uwar gidan Gwamnan Sakkwato Mariya Aminu Waziri Tambuwal da hadin guiwar Mintreach PR sun shirya taron karawa juna sani irinsa na farko ga manema labarai da suka kunshi jaridu da talabijin da radiyo da kafofin sada zumunta na zamani don a fito da wasu hanyoyin da za a bi don kawar da cin zarafin jinsi a Sakkwato. 

Mariya Tambuwal wadda ake kira Uwar marayu ta ga dacewar yin wannan hadaka don kawar da cin zarafin jinsi saboda tausayinta da kulawarta da jama’arta musamman mata da ba su  da wata gata sai Allah.


Cin zarafin mata wanda aka fi sani da cin zarafin jinsi abin bacin rai ne dake taba lafiya da hankalin duk wanda ya fada cikin kaddarar,  Manya da yara maza suna haduwa da musibar amma dai tafi yawaita ga mata a duniya gaba daya.

Daya daga cikin mahalarta taron ke gabatar da jawabi.

Taron ya fadakar da manema labarai a jiha yanda matsalar ke tafiya kamar wutar daji akwai bukatar su sanya basirarsu wajen wayar da kan al’umma su guji aikatawa, wanda aka yi wa kuma ya nemi hakkinsa a hanyar da ta dace.

Daya daga cikin mahalarta taro ke gabatar da jawabinsa.
Hajiya Ubaida Muhammad Bello a lokacin da za ta shiga dakin taro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *