Spread the love

 
A tashar mota dake unguwar Kwanawa cikin karamar hukumar Dange Shuni a jihar Sakkwato direban motar sufuri a ranar Lahadi data gabata ya gano wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojinsa da zai dauka zuwa Kano.


Direban an yi garkuwa da shi ne a saman hanyar Kankara cikin jihar Katsina a lokacin da yake dawowa daga Kano kusan wata biyu da suka wuce, direban ya kwashe sati uku a tsare kafin a sake shi da aka biya kudin fansa. 


Wanda ake zargi ya shiga hannu ne a lokacin da ya zo shiga mota zai je Kano, ba tare da saninsa ba direban motar da zai shiga sun taba garkuwa da shi, ya gane shi domin abun bai dauki lokaci ba da ya ganshi ne bai tsaya komi ba ya sanar da shugabannin kungiyar direbobi ta NURTW kamar yadda wata majiya ta sanar.Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jiha DSP Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kuma ana kan bincike. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *