Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Cin zarafin jinsi cuta ce dake addabar al’umma kuma ba wata kasa da ta tsira, kan haka kungiyar kare hakkin mata ta duniya ta tari aradu da kai don ganin ta taimakawa mata ga wannan matsalar dake addabarsu tun kafin  lokacin shigowar cutar Korona.

Mahalarta taro suna sauraren bayani a wurin manyan baki.

Malama Nafisa Adamu Gurori ta furta hakan a wurin taron wayarda kan al’umma kan cin zarafin jinsi da kungiyoyi suka shirya karkashin jagorancinta a satin da ya gabata cikin zauren makarantar kimiya da fasaha ta Ummaru Ali Shinkafi a Sakkwato ta ce a Nijeriya kididdiga ta nuna kashi 30 na mata dake tsakanin shekara 15 zuwa 49 suna fuskantar kokarin keta masu haddi.

 Malama Nafisa ta kara da cewar a  wani rahoto da cibiyar kasa da kasa ta fitar ta ce a lokacin kullen Korona an samu yawaitar cin zarafin jinsi a jihar Lagos da Ogun da  babban birnin Abuja, a tsakanin watan Maris zuwa Afirilu kawai an samu bayani a wadan nan jihohin cin zarafi ya karu daga samun tuhuma guda 60 ta koma 238, kashi 297 aka samu kari.

Malama a jawabinta na maraba da baki ta zayyano wasu hanyoyi da yakamata a bi domin magance matsalolin cin zarafin jinsi musamman mata ta hanyar taimakawa wadanda suka fada cikin kaddarar a tsaya masu har sai an kwato hakkinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *