Daga Muhammad M. Nasir

Jam’iyar APC ta kira taron gaggawa na majalisar zartawar jam’iyar waton NEC,  an shirya gudanar da shi a ranar Talata mai zuwa 8 ga watan Disamba.

Taron majalisar tun bayan wata biyar da aka gudanar da shi a fadar shugaban kasa ba a sake yi ba sai yanzu da aka saka lokaci.

Mataimakin Sakataren yada labarai na jam’iyar Yakini Nabena ya fitar da bayanin a wannan daren na Lahadi ya ce zaman zai kalli matsayar jam’iyar da kuma in da za a sa a gaba.

Jawabin ya ce za a tura sakon gaiyata ga wadanda abin ya shafa amma za a yi shi ne a yanar gizo tare da kiyaye sharuudan kula da cutar Korona, a ranar da za a yi da 11 na safe ne a babban zauren fadar shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *