Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Barista Hafsat Sahabi Dange shugabar kungiyar Muryar Mata daya daga cikin masu kare hakkin mata a jihar Sakkwato ta shawarci hukumomi a kasa su samar a da cibiyoyin kare hakkin mata a kananan hukumomi hakan ne zai sanya kiyayen hakkin mata da daukar matakin wadanda suka ci zarafin mata a Nijeriya

Barista ta yi wannan kalamai ne a wurin taron kungiyar daura mata saman hanya da hadin guiwar kungiyar matan Turai da ma’aikatar lamurran mata ta Nijeriya  a satin da ya gabata a wani bangare na bukin yaki da cin zarafin mata na shekarar 2020, a kwanaki 16 da aka ware, ta ce rashin samar da cibiyoyin ke sanya kafin a zo da mai laifi a babban birnin jiha an lalata hujjoji da shedun da ake da su na cin zarafin da aka yiwa mace.

“Don haka mu san abin da muke yi don Allah ana ganin ba mu da ilmin addini ba haka ba ne mun san abin da yakamata muna da tausayi; tausayinmu da sanin yakamatarmu mun ninka na maza.” A cewar Barista Hafsat Dange.

Ta shawarci mahaifa da mutanen gari su rika furta kalaman tausayawa ga wadanda kaddarar cin zarafi ta rutsa da su a rika furta masu kalmomin “muna tare da ke, za mu taimaka miki abin da ya faru ba laifinki ba ne, da suran kalmomin tausayawa yarinya da ba ta kwarin guiwa ta fito ta fadi abin da ya faru da ita.

“Mu kadai ne za mu yi wa kanmu magani ba wanda zai yi mana wannan yaki, ina jinjina ga wadanda suka shirya wannan taron.” In ji Hasfat.

Ta ce cin zarafin mata a duniya ba wani sabon abu ba ne yadda miliyoyin mata suka fada cikin matsalar, yana kan gaba a cikin cin zarafin mutane, ana daura laifi ga wadda aka ci zarafinta, da a tsaya ganin laifi mi zai hana a hada kai domin kawar da matsalar cin zarafin mata a cikin mu’amala ta rayuwa.

Shugabar taron Hajiya Nafisa Adamu Gurori ta godewa mahalarta taron tare da jinjina masu da hadin kan da suka bayar na ganin an yi nasara a taron na yini daya mai taken, Ganin laifin wadanda aka ci zarafinsu: Kira a dauki mataki ta hannun al’umma a wannan lokaci na cutar Korona.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *