Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Mohammed Matawalle ya yi Allah wadai da irin matsayin da gwamnonin jam’iyar PDP a shiyyar Kudu maso Kudu suka soki gwamnatinsa akan batun hakar zinari, duk da cewa suna jam’iyya daya.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takardar bayani wadda mai ba da shawara na musamman, da wayar da kan jama’a, kafafen watsa labarai da sadarwa, Alhaji Zailani Bappa ya sawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Bayanin ya kara da cewa, gwamna Matawalle ya soki gwamnonin na PDP ne saboda sunki su fahimta bisa ga bayanin da ya yi wa mutane game da matsayar jihar Zamfara kan zinariya.

“Ina fuskantar mummunan suka ‘yan kwanakkin nan daga wasu abokan aiki na Gwamnoni kuma yan jam’iyyata ta PDP wanda har yanzu abun na daure mani kai. Misali, Gwamnonin Kudu-maso-Kudu da suke zargina a kafafen yada labarai Gwamnoni ne na PDP kuma su ne mutanen da suka haifar da rikici a kan abin da ake kira Zinaren Zamfara”. inji shi.

Ya koka kan cewa duk wayan nan korafe korafen nasu an shirya su ne kan karya kuma da gangan domin son cin zarafi.

Matawalle ya yabawa gwamnatin tarayya ta APC da ta warware wannan matsalar,
“Abin mamakin shi ne, Gwamnatin Tarayya ta APC wacce ke da cikakkun bayanai game da batun hakar zinare ne suka fito don kare ni a cikin wannan yanayi. A matsayina na abokin aikin PDP, na yi tsammanin gwamnonin yan jam’iyyata na kudu maso kudun za su fara tuntuɓata kuma su gano yadda lamarin yake kafin su bayyana manufar su a kafofin watsa labarai.

“Ina yaba wa shugaban kasar Tarayyar Najeriya, Mai girma Muhammadu Buhari saboda ba da goyon baya ga kokarin da muke yi na tsara bangaren tattalin arziki a jihar don kauce wa amfani da ma’adanan don inganta rashin tsaro a jiharmu ta Zamfara, ” Gwamnatin Tarayya na bayar da lasisi ga Kamfanoni da suka cancanta don yin aiki a bangaren ma’adanai a jihar.

“Babban kamfani da ke da jarin biliyoyin nairori mallakar wani dan Najeriya ne daga jihar Anambra. Kuma ina mamakin ina aka samo cewar jihar Zamfara ce keda mallakar ma’adanan gwal. Kamar yadda yake a yanzu, Gwamnatin Jiha ba ta da hannu a duk wani aiki na hakar ma’adanai a cikin jihar saboda tsarin mulki bai ba mu ikon yin hakan ba, ”in ji Matawalle.

Matawalle ya kuma zargi gwamnonin PDP a matsayin wadanda ke da alhakin Gwamna David Umahi na Ebonyi ya bar jam’iyyar su zuwa abokiyar hamayyarta ta APC.

Gwamnan ya ce ya yaba wa Gwamnan saboda yanke shawarar da ya yi na barin PDP, maimakon yin Allah wadai da shi saboda kowa yana iya zama ne kawai a gidan da yake jindaɗi.

“Idan wannan dabi’ar ta haifar da mummunan bakin jini a tsakaninmu ta ci gaba ba tare da yin gyara ba babbar jam’iyyarmu ba za ta kara samun karbuwa ba yayin da muke ta tunkarar zabe a shekarar 2023.

“Ina kira ga Gwamnonin Kudu-maso-Kudu da guji yada abinda basuda ilimi akan sa, kuma su tallafawa mutanen su, su yi aiki da matatun mai na zamani kamar yadda doka ta tanada tare da fitar da mutanensu daga tsoro maimakon zama a baya da fara bin inuwa,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *