Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Shugaban hukumar  Zakka da Wakafi na jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ce barin Shari’a ne ya sanya mata cikin matsalolin da suke ciki.

Yayi wannan kalamin ne a wurin taro kan cin zarafin mata da aka gudanar a makarantar kimiya da fasaha ta Umaru Ali Shinkafi a Sakkwato.

Shugaban ya ce shi bai goyi bayan fallasa wanda ya yi wa Mace fyade ba, “Don mi za a nuna Mace an yi mata fyade, ban goyi bayan in an yi wa mace fyade a fadi ba, domin in fallasar ba uwar da ke bari danta ya auri yarinyar, in kaddara ta faru a rufa asiri domin maza ba su son wadda aka yiwa fyade.

“Hukuncin wanda ya yi fyade Allah ya fade shi a Alkur’ani, addini yana son rufin asiri. In ji Maidoki.  

Hajiya Maryam Maiyaki babbar jami’a ce a hukumar tsaftace finafinnai da hotunan bidiyo a Sakkwato a jawabinta wurin taron ta kalubalanci Malam kan maganarsa ta ce “Malam ya ce mu zo mu rafa asiri ta yaya ne ga wata yarinyar ‘yar shekara 12 wani ya yi mata fyade a gaba da baya kwananta uku a some ba ta san in da take ba, wanda ya yi haka makwabcinsu ne daga ta kai naman suna ya kamata wata ce ta ji ihunta ta kira jama’a aka ceceta.

Ta ce “Duk wanda yace maka kar ku yi magana in an yi wa ‘ya’yanku fyade kar ku yarda don ku ne za ku zama cikin matsala shida ‘ya’yansa suna gida zai yi masu aure.

“Talakawa ake cuta kar mu yi magana, in kun ga wadda aka yi wa fyade ku gayamin zan tsaya mata na dauki nauyin abin da aka yi mata da kwato hakkinta, cutar da ake yi mana da ‘ya’yanmu mata ya yi yawa muna shiru.” in ji ta.

Jami’ar ta ci gaba da cewa akawai wata da wasu suka bata har ta yi ciki amma ‘yan sanda suka kulleta ba tare da wadan da suka yi mata  ba. 

“Sai wani ya ce maku kar ku yi magana, ku yi ku kara da ihu, ba wani namiji da ya isa ya yi wa mace fyade a yi shiru karya ne.” a cewar Hajiya Maryam. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *