Spread the love

Gwamnatin Nijeriya za ta bude iyakokinta nan ba da dadewa ba, an rufe bododin ne a shirin da gwamnati take da shi na magance haramtattun ababe da ke shigowa da su cikin kasa Ministan Kudi da tsare-tsaren cigaban kasa Hajiya Zainab Ahmad ta sanar da hakan. 

Nijeriya ce mafi girman kasa da samar da tattalin arziki a Afirika ta Yamma, a watan Agusta na shekarun da suka gabata ta rufe iyakokinta na tudu da zimmar tsaftace shige da fice musamman kan miyagun kwayoyi da makamai da bunkasa harkar noma a kasar. 

Ministar tana karba tambayoyi kan maganar rufe boda bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta kasa da shugaba Buhari ya jagoranta ta ce kwamitin da aka kafa kan su duba nasarorin da aka samu, sun amince a sake bude bododin Nijeriya don haka shugaban kasa zai sanar da lokacin bude iyakokin..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *