Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta chafke wani shahararren barawon Mota mai suna Sirajo Ibrahim dake anguwar gidan dare jihar sakkwato, bayan sunki karbar cin hancin da yaba su harna naira dubu dari biyu da hamsin (250,000)

Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa dake a hedikwatar yan sanda dake Gusau babban birnin jiha, yace tawagar jami’an hukumar da suka kunshi yan sandan kwantar da tarzoma da masu yaki da ayukkan ta’addanci wadanda aka girke a wani shingen Bincike dake Tazame akan hanyar Gusau zuwa Zaria ne suka chafke wanda ake tuhumar.

SP Muhammed Shehu ya kara da cewa sun kama wata Mota mai kalar Siminti, kirar Toyota Matrix mai Lamba ABC 584 AP wadda wani mai suna Sirajo Ibrahim na shiyar Gidan Dare da Sakkwato ya tuko domin kaita wani gari.

” Wanda ake tuhumar ya kasa yiwa jami’an yan sandan bayanin yadda ya samu motar, a maimakon hakan sai yayi yunkurin baiwa jami’an sandan cin hanci na Naira Dubu Dari Biyu da Hamsin lamarin da ya kara tsananta zargi akan shi da yakai ga suka chafke shi, suka hannun tashi ga sashen binciken manyan laifuka na Rundunar.

“A wurin binciken, wanda ake zargin ya bada tabbacin cewa, wani daga cikin yan gungun su dake satar motochin, mai suna Abdullahi ne mazaunin Abuja ya sato Motar daga Kasuwar Wuse dake Abuja a ranar 15 ga watan nan na Nuwamba wanda yanzu haka ya gudu.” inji shi.

A ta bakin jami’in hulda da jama’a na yan sandan, wanda ake tuhumar, Sirajo Ibrahim ya shaida cewa yana kan hanyar shi ne ta kai Motar zuwa ga wani Adamu dake jiran shi a Magama, wato kan iyakar Nigeria da Nijar a jihar Katsina.

Ya kuma bada tabbacin cewar wannan ita ce Mota ta Uku da yake kaiwa a Magama, kuma anyi yarje jeniyar biyan shi naira dubu talatin ne na kai Motar, yana mai cewar baida masaniya akan yadda aka samo Motar, saboda a cewar shi Abdullahin ne ya kawo mashi Motar a Kaduna ya kuma bukachi ya kaima Adamu ita a Magama kamar yadda ya kai mashi a lokacin da ya gabata kafin a wannan karon rana ta batar mashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *