Spread the love


Daga Muhammad M. Nasir. 
Sardaunan matasan jihar Sakkwato Alhaji Mujittaba Isa Helele ya yi kira ga matasa su zama jekadu nagari a cikin al’umma domin kawo sauyi da cikin gaban jama’a.


Sardauna a zantawarsa da manema labarai satin da ya gabata ya bayyana takaicinsa kan yadda matasa suke gudanar da rayuwarsu ba tare da kula ba.


“a yanzu matasanmu ba su san masu sonsu ba, kuma ba ruwansu da gina rayuwarsu ta zama mai inganci da za ta taimaki jama’a, wanda haka bai kamata mutum ya rika tafiya ido rufe ba tare da sanin makomar sa ba” a cewar Sardauna. 


Ya cigaba da cewa matasa su ne ginshikin cigaba lokaci ya yi da za su yi karatun ta natsu su rungumi shugabanni masu sonsu da za su taimaki rayuwarsu ta inganta ta hanyar samar musu da hanyoyin dogaro da kai. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *