Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Zamfara yayi nasarar kubutar da mutane 11 da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba ta hanyar kokarin da gwamnatinsa ke yi na sasanci da yan ta’adda.

A wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji ya rabawa manema labarai a Gusau ta ce gwamnan ya amshi mutanen da aka sace a gidan gwamnati, dake Gusau babban birnin jihar.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, maza 10 ne kuma mace daya daga karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar ta zamfara.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa ba za ta huta ba har sai an samu cikakken zaman lafiya a dukkan sassan jihar.

Gwamnan ya ci gaba da bayanin cewa, yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa da akayi da ‘yan ta’addan da suka tuba zai ci gaba a jihar, yayin da wadanda ba su tuba ba za su gamu da fushin gwamnati.

Da yake yiwa gwamna jawabi tun da farko, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran ya shaida wa gwamnan cewa, an saki wadanda lamarin ya rutsa da su ne sakamakon shirin zaman lafiya na gwamnan da kuma bin wani taron masu ruwa da tsaki da gwamna Matawalle ya kira tare da dukkan masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar ta Bukkuyum.

Wadanda aka ceto din sun nuna matukar farin ciki da godiya ga Gwamna Bello Matawalle wanda suka bayyana a matsayin mai samar da zaman lafiya da kuma gina hanya mafi sauki tsakanin dukkanin bangarorin mutane a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *