Spread the love

Kasar Nijeriya ta sake tsunduma cikin matsin tattalin arziki a karo na biyu kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa NBS ta sanar a jiya Assabar GDP na Nijeriya ya rikito da kashi 3.63 a cikin zangon karshe na 2020.

Wannan shi ne karo na biyu da tattalin arzikin yana fadawa cikin wannan matsalar hakan ta faru a 2016.

Fadawa cikin matsin tattalin arziki yana nufin Za a rasa aiki ga masu aikin kamfunan kasuwanci, kudin da mutane ke samu za su rage sosai, gudanar da rayuwa zai sauya Matuka.

Yadda farashin abinci ya yi tashin gwauron zabo wata damuwa ce mai cin gashin kanta domin talakawa ba su iya sayen abincin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *