Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce ba zai goyi bayan mutanen da ke ta kokarin sai sun murkushe tasirin siyasar tsohon gwamnan jihar Lagos Asiwaju Bola Tinubu ba.

Ya furta hakan a wurin bukin cikarsa shekara 60 a birnin Ado Ekiti tsohon gwamnan ya bayyana Tinubu mutum ne mai daraja a yankin yarbawa da Nijeriya gaba daya.

Ya ce duk da yana da bambancin jam’iya da Tinubu amma ba zai shiga cikin mutanen da ke kokarin ganin bayansa ba, yakamata mutane su rika godewa wadanda suka yi masu alheri.

Managarciya ta fahimci ana yunkurin kassara siyasar Tinubu don a tabbatar bai yi tasiri ba a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *