Spread the love

Wasu jigogin jam’iyar PDP sun bayyana damuwarsu kan tattaunawar sirri da gwamnonin APC suka yi da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan awowi kadan bayan ficewar gwamnan Ebonyi daga PDP.

Gwamnonin da suka yi tattaunawar suna karkashin jagorancin gwamnan Yobe shugaban riko na jam’iyar Mai Mala Buni da gwamnan Kebbi da Jigawa da Ebonyi, an yi ta ne a gidan Jonathan dake Abuja.

Wata majiya ta tabbatar cewa jam’iyar APC na zawarcin Jonathan ne.

Mataimakin Sakataren yada labairai na jam’iyar Yakini Nabena ya tabbatar da shugabanninsu na yunkurin shigo da Jonathan jam’iyarsu hadi da wasu gwamnoni da jagorori a Nijeriya.

Ya ce siyasa magana ce ta yawa ba suna tursasawa mutane ba ne, suna rokonsu ne kawai kuma suna yin haka ne kan zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *