Muhammad M. Nasir.


Honarabul Abdullahi Hassan dan siyasa ne a jihar Sakkwato ya bayyana makusantan gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal basa tare da shi kuma ba su gamsu da salon mulkinsa ba.


Honarabul ya bayyana hakan a turakarsa ta facebook ya ce “Maigirma Gwamna ina sanar da kai 80% da kake gani kusa da kai basa tare da kai kuma ba su gamsu da salon mulkin ka ba, suna biyar ka ne kawai saboda wannan kujerar, dazarar ka gama zaka sha mamaki fiye da Wamakko da Bafarawa wadanda duniya ta shedi sun fika yin abin azo a gani.” a cewarsa. 


Ya cigaba  da cewa babban abin da ke bashi haushi munafurcin  matasa na nuna ayukkan Tambuwal  hubbasar kamar irin na shugaban karamar hukuma.

“Babban abin da ya tayarmin da hankali shi ne wani lokacin da muke tattaunawa da Abu Shekara a radio yake fadawa Duniya cewa “Ai gine-gine ba shine cigaba ba, a yanzu wannan lokacin jahiliya ne” sai na tambayeshi me yake kaishi Dubai da sauran kasashen turawa ya dauki hoto ya saka kafar sadarwa?” a cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *