Spread the love


Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Muhammad Buhari ta ce  tana kokarin mallakar sama da kadada dubu 720,000 daga jihohi daban-daban don inganta amfanin gona a Nijeriya.


Ministan Noma da Raya Karkara, Alhaji  Sabo Nanono ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a wata ganawa da ya yi da shugabannin gudanarwa  manyan jami’an  ma’aikatar aikin gona ta tarayya da raya Karkara a birnin  Abuja.


Ya ce ma’aikatarsa ​​ta  tanadin fili tsakanin kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha da nufin bunkasa bangaren noman kasar nan. Gwamnatin Tarayya za ta mallaki kadada dubu 720,000 daga dukkan jihohin 36.


Ministan ya kara da cewa    “A yanzu haka, ma’aikatar ta dauki kwararan matakai na sanya tsarin binciken aikin gona, da samar da kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha don amfanin aikin gona, da kuma inganta ayyukan gona da hadin kai a duk ƙasar.

“Tsammani mu shi ne tura ingantattun iri, fadada yankin noma da tallafawa ayyukan noma a kasar.”.


Gwamnatin tarayya koyaushe suna maganar bunkasa aikin noma amma har yanzu bai sauka saman takarda ba.  

Dubi yadda abinci farashinsa ya yi tashin gauron zabo, manoma suna noma ba tallafin kirki na a zo a gani kuma yanzu an fito da sabon shiri sai  dai a zuba ido a gani.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *