Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

 Matar Gwamnan Sokoto Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal  ba ta halarci bukin babban Dansa Najib Aminu Waziri,  musamman kasaitaccen bukin cin abincin dare da aka shirya wanda ba a taba shirya irinsa a tsari da kashe kudi a tarihin jihar Sakkwato ba.

Bayan kamala bukin ne hankalin mutane wadan da suka halarci wurin da wadan da hotunan buki ya riska suka fahimta tare da tabbatar da lalle bas u ga fuskarta ba, daga nan ne aka shiga neman dalili ganin yanda take da ango.

Jami’in hulda da jama’a na matar Gwamnan Alhaji Amiru a zantawarsa da Managarciya ya ce rashin zuwan nata ba wata matsala ne ba domin a lokacin da ake bukin tana Abuja ba ta da lafiya amma ta turo wakilanta a wurin bukin gaskiya ba wata matsala. 

Mutane sun yi ta cece-ku-ce kan rashin halittarta amma yanzu an ji uzurin da ya kamata. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *