Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamna Bello Muhammed na jihar Zamfara ya karbi tsoffin kansiloli 69 da sakatarorin kananan hukumomi 14 da suka watsar da tsohon gwamna Abdulaziz Yari da APC, zuwa jam’iyyar PDP.

Sauya shekar da wadanda suka yi aiki a matsayin zababbun Kansiloli tsakanin shekarar 2012, 2015 zuwa 2019 bi da bi sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP karkashin inuwar kungiyar ta tsofaffin kansiloli reshen jihar ta Zamfara.

Shugaban tsofaffin kansilolin, Alhaji Tukur Muhammed Magami ya ce shawarar da suka yanke na barin tsohon maigidan nasu ya biyo bayan tsananin imanin da suke da shi game da salon shugabancin Gwamna Bello Muhammed Matawallen Maradun, musamman wajen yaki da rashin tsaro da samar da kyakkyawan yanayin siyasa a cikin kowa ne sassan jihar.

Ya ce, wannan gwamnatin da Matawallen Maradun ke jagoranta an tabbatar da cewa gwamnati ce ta kowa domin ba ta cin mutunci ko barazanar siyasa ga mambobin wasu jam’iyyun siyasa a jihar.

A cewar shugaban dandalin, irin wannan gwamnatin na bukatar haduwa tare da tallafawa kowa da kowa domin ta ci gaba da samar da ribar dimokiradiyya ga dukkan ‘yan jihar.

Ya ba da tabbacin cewa dukkanin mabiyansu da magoya bayansu har da danginsu suna da ra’ayi iri daya da sanarwa ga gwamnatin Matawalle kuma sun yanke shawarar komawa PDP tare da bada tabbacin cewa zasu ci gaba da bada goyon bayan su domin ci gaban jihar.

Hakazalika, kakakin tsofaffin sakatarorin kananan hukumomin 14, Alhaji Saadu Mayana ya bayyana cewa Matawalle ya sauya jihar zuwa ga mataki na gaba.

Yace wannan hada kai tsakanin su da kansilolin ya nuna cewa gwamnan mutun ne mai son ci gaban jama’ar sa.

Ya kara da cewa a madadin tsofaffin sakatarorin kananan hukumomin 14 na jihar, mun yanke shawara baki daya mu shiga gwamnatin PDP a jihar karkashin Matawalle don kyautatawa Zamfara.

A nasa martanin, Gwamna Bello Mohammed Matawalle wanda ya bayyana farin ciki yayin karbar sabbin masu shigowa PDP ya lura cewa kiran nasa zai kasance koyaushe ga duk masu kyakkyawar ma’ana a jihar don su bi shi don ciyar da jihar gaba.

Yace ya yanke shawarar sauya jihar zuwa wani matsayi mai matukar kima da za a iya aiwatar da shi cikin sauki idan kowa ya bi shi a wannan batun, musamman wajen yaki da rashin tsaro.

Gwamnan ya ce, kofofin sa za su kasance a bude ga kowa ya kasance tare da shi domin fitar da hanyoyin da suka dace don ci gaban jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *