Spread the love

Tashin gauron zabon da garin Fulawa ya yi yana cikin abin da ya kara kawo matsi gamutanen Nijeria, domin mutanen kasashen waje ne ke juya kasuwar garin Fulawa a kasar. 

Mutanen daake amfani da fulawa da masu Burodi a gida sun koka kan tsadar garin Fulawa a wannan lokacin,  wasu jihohi masu burodi na cikin yajin aiki don nuna rashin gamsuwarsu da yanda farashin  wasu kuma  Karin farashin biredi suka aiwatar, biredi  yana cikin abincin da yawan mutanen Nijeriya ke ci mi kake ganin ya janyo haka?

Tabmayar da aka yi wa  Anurag Shukla  manajin Darakta na kamfanin Fulawa Crown mallakar Kungiyar Olam a tattaunawar da aka yi da shi ya bayyana irin hobbasar da kungiyarsu ke yi na tallafawa manoman Alkama na gida Nijeriya.

Babban abinda ke bayyana farashin garin fulawa shi ne yanda Alkama take a kasuwa, an dade ana shigo da Alkama a kasar nan don haka farashinta ya dogara da yadda harkar canjin kudin Nijeriya take da ta kasashen Turai, a watan Maris na 2020 da cutar Korona ta fara kasuwanci ya tsaya, anan ne aka samu koma bayan kudin Nijeriya, Naira ta tashi daga 337 a 20 ga Fabarairu ta koma 455 a 20 ga  watan Yunin nan da ya gabata, an samu ci baya da kusan kashi 35, ga masu gyaranta da karfinsu an samu kari a wurin da kusan kashi 40 cikin kashi 24 da suke karba a baya, wannan ya haifar da tsadar Fulawa, da kashi 15,  a cikin yanayin ne kayan hada burodi suka tashi kamar suga ta yi kari da kashi 30 Yis da kashi 17.  Duk da karewar darajar naira da rashin tabbas a harkar canjin kudi  tsawon shekara biyu da suka wuce masana’antun Fulawa sun kokarta ba su Kara kudin Fulawa ba domin tsadar Alkama.

Masana’antun gurzar Alkama suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Nijeriya don suna iya Samar da aiki ga mutane sama da miliyan 10,  Kan haka muke ta kokarin mu ga dai ba su durkushe ba. A bangarenmu muna duba yiwuwar saka jarinmu a fannin cigaban zamani don jama’a su cigaba da amfana ga abubuwan da muke samarwa hakan zai sa masayanmu su samu abu mai kyau da saukin farashi. 

Sama da shekara 10 da suka wuce kamfanin Olam ya saka hannun jarin sama da biliyan 300 don Samar da Kuma daukaka darajar masana’antun Fulawa a Nijeriya. Ta hanyar wannan hannun jarin za mu tabbbatar da an samu cin gajiyar abin, a cikin dokar shigo da Alkama  cikin kasa domin Fulawa ta yi rahusa a wurin mai saye. 

Duk da farashin garin Alkama ya yi sama manoman Alkama a Nijeriya suna kokawa kan  yadda kamfanoni ke yi masu rashin adalci, mafiyawan masu kamfanonin ‘yan kasashen waje ne. 

Wani bangare na koken manoman, ba su samun tallafin da suke bukata a lokacin da bayan noman da suke yi. Su kuma Kamfanonin suna koka yadda Alkamar Nijeriya ba ta da inganci amma Kuma sun ki tallafawa manoma su samar da iri Mai inganci da suke bukata. Haka ma suna ganin ana sanya tsada ga farashin Alkamar gida. Mi zaka ce Kan wannan?Shekarru da dama da suka wuce Kungiyar Masana’antun Fulawa ta Nijeriya(FMAN) abokan hulda ne da Kungiyar manoman Alkama ta Nijeriya(WFAN), mun Samar da budaddiyar kasuwa ga manoma, da tabbacin za a saye alkama ga manomi da farashi sama da Kashi 50 ga yanda ake sayenta  a kasuwar duniya, amma wannan abin zai dauki lokaci kafin manoma sun inganta alkamarsu mu fahimci hakan tun farko. 

Mambobin FMAN ba su kokawa Kan ingancin Alkama suna karbar duk yanda manomi ya ba su, abin lura anan Alkamar gida ba ta isa a wurin cike gibin wadda ake shigowa da ita.A matsayinka na daya daya cikin masu ruwa da tsaki a wannan haujin, mi kake ganin za a yi ga manoman Alkama don su samar da Mai inganci da zai sa su ci amfanin abin, Kuma ya kake ganin in da gwamnati za ta shigo ta karfafa Samar da Alkama a kasar Nijeriya.?

Kungiyar FMAN ta kirkiro cibiyar cigaban bincike ta yankin Chadi domin kawai bunkasa noman Alkama daban-daban, haka Kuma ta kirkiro shiri a 2019 zaburar da girman shuka, manoma 400 aka sa a cikin shirin, Muna da zimmar Kara fadada Shirin. Abu mai muhimmanci da yakamata mu fahimta a nan shi ne tsiren  Alkama abu ne mai son hutu, shi ne ya sanya yake da wahalar girma yadda ake so a Nijeriya.

Kwanan nan  gwamnatin tarayya da bankin kasa CBN sun kaddamar da bayar da tallafin ga manoman Alkama don bunkasa haujin wannan abu ne Mai kyau Kungiyarmu a shirye take ta goyi bayan wannan hobbasar. 

In dai ana son wannan Shirin ya yi nasara yana bukatar tsari da zai daure har gaba, a rika tallafawa manoma da kayan noma da wurin noman rani da iraruwa masu matukar inganci da takin zamani da sauran kayan noma, tallafin kudin noma da horas da manoma a karshe in ka cire amfanin gonarka, kasuwa na jiranka, hakan kawai zai bunkasa haujin.

Nasarar Shirin tana rataye ga bude kofa ga masu ruwa da tsaki da suka hada da masana’antu da manoma, gwamnatin jihohi da tarayya da bankin kasa su mayar da hankali ga gina haujin, rayuwar mutane miliyan 10 da suka dogara ga harkar Fulawa a tsare ta don cigaban Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *