Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Kwamishinan raya Karkara da cigaban al’umma na Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya dauki nauyin bikin auren ma’aurata 50 a karamar Hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Da yake jawabi jim kadan bayan kammala daurin auren wanda ya gudana a fadar Maimartaba Sarkin Tsafe, Abdullahi ya ce wannan karimcin na nufin tallafawa marasa karfi ne da wadanda ke fama da fashi da makami da sauran matsalolin tsaro, a yankin sa.

Ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar ne daga gundumomi 17 na Tsafe kuma akasarinsu wadanda ke fama da hare-haren ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro ne.

Kwamishinan ya ce “Mun gano cewa yawancin Zawarawa da matan aure suna bukatar taimako game da wannan iftila’i dake faruwa a wannan jiha da sauran wasu jihohi na arewa maso yammacin Najeriya.”

Ya yaba wa mai martaba Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa, da malaman addinin Musulunci a yankin kan karfafa masa gwiwar daukar nauyin daurin auren.

“Mun yi imanin cewa wannan tsoma bakin za su taimaka wajen rage zina da sauran munanan halaye a cikin al’umma.

Ya kara da cewa “Wannan ya dace da tsarin tafiyar da gwamnati mai ci yanzu a jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle don magance matsalar tsaro da sauran matsalolin rayuwa.”

A nasa jawabin, Gwamna Matawalle ya yaba wa Kwashinan bisa ga wannan taimako da yayi na daukar nauyin wannan auren na ma’aurata har guda hamsin.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Magarya, ya bukaci manyan jami’an gwamnati, masu rike da mukaman siyasa da sauran masu hannu da shuni da su zage damtse wajen tallafawa mabukata.

“Wannan ya yi daidai da manufofin gwamnatinmu don samar da taimako ga masu karamin karfi a cikin al’umma.

“Muna godiya da wannan kokarin da daya daga cikin kwamishinonin mu ya yi; muna fatan wannan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da sauran matsalolin zamantakewar jihar, ”inji shi.

Matawalle ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da addu’o’i na musamman don neman taimakon Allah don kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Sarkin Tsafe Alhaji Muhammadu Bawa ya yabawa kwamishinan kan saukake halin da matan aure da matan aure ke ciki, ya kuma bukaci ma’auratan da su rungumi hakuri kuma su zauna lafiya don samun iyalai na gari.

Tun da farko, a nashi jawabi Shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Buhari Kaura, ya ce an kashe sama da Naira miliyan 25 don bikin auren.

Kaura ya ce an ciro wadanda suka ci gajiyar ne daga dangin da ba su da karfi a duk sassan jihar.

Ya ce an baiwa kowanne daga cikin ma’auratan kayan aikin gida, kayan daki, sutura da kayayyakin abinci, hakama yace an biya N20,000 a matsayin sadaki a kan kowacce daga cikin amare 50.

Matan guda 50 sun samu wakilcin Gwamna Bello Matawalle, yayin da mazan nasu 50 suka samu wakilcin Sanata Kabiru Marafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *