Spread the love

Jagoran jam’iyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya shawarci dukkan gwamnoni da aka zaba a karkashin jam’iyarsu da su soke Fanshon tsoffin gwamnoni da mataimakansu kamar yadda dan uwansu gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya aiwatar.

Ya ce shirin gwamnan na hana cigaba da bayar da Fanshon gwamnoni da mataimakansu mataki ne abin yabawa ne da zaburarwa. 

Gwamnan Lagos a ranar Talata ya mika kudirin doka barin baiwa tsoffin gwamnoni da matakansu Fansho don rage kashe kudin gwamnati ga majalisar dokokin jiha. 

A ranar Laraba jagoran ya yabi  Sanwo-Olu ga wannan lamarin a turakarsa kuma ya shawarci gwamnonin APC su yi kamar haka.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *