Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Fitacciyar Jaruma a masana’artar shirya finafinnai a Nijeriya watau Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta ce babu wanda ya kama ta sannan babu wanda ya yanke mata hukunci a gidan yari, kuma ‘yan sand aba su kama ta ba.

Jarumar ta bayyayana hakan a shafinta na Tweeter bayan da bayanai ke ta yaduwa a kafafen sada zumunta cewa an kama ta kuma an gurfanar da ita a Gaban kotun shariar Musulunci, kan zargin batancin da aka yi wa fiyayyen halitta Muhammad S.A.W.  

Freedom Radiyo Kano ta ruwaito jarumar na cewa ita bata da masaniya da inda labarin ya samo asali, don haka ta yi kira ga mutane da su daina yada labarin Karya marasa tushe da makama.

A makon da ya gabata ne dai Rahama Sadau ta wallafa hotuna a tweeter dake nuna bayanta a bude inda mutane suka yi ta rubdugu da tofin Allah tsine duk da wasu na caccakar jarumar wasu kuma na kare ta.

Sai dai mafi yawan wadanda suka fito daga kudu suna yabon jarumar ne, yayin da wadanda suka fito daga arewacin Nigeriya suke sukarta, inda wani ya yi batanci ga manzo S.A.W a kasan hotonta lamarin da ya jawo cece kuce musamman daga arewacin Nigeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *