Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziya ga gwamnatin jihar Kaduna da mutanen jihar kan rasuwar tsohon gwamnan jihar Alhaji Balarabe Musa ya bayyana rashi ne da mutanen Nijeriya suka yi musamman yadda margayin ke kokarin kwato hakkin takakawa. 


Shugaba Buhari ya yaba jajirewar Alhaji Balarabe Musa kan kokarinsa na adawo saman mulkin Dimukuradiyya da kiraye kiranyensa na a yi mulkin hadin kai.


A jawabin da mai baiwa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce margayin ya taka rawa wurin ganin an samu gwamnati mai adalci da ci gaba koyaushe za a rika tuna shi da halayensa nagari.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *